On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Farashin Litar Fetur A Najeriya Ka Iya Kaiwa 680 Zuwa 710 - Dillalai

‘Yan kasuwar man fetur sun yi hasashen cewa farashin man fetur zai tashi tsakanin Naira 680 zuwa Naira 720 a cikin makonni masu zuwa idan dala ta ci gaba da kasancewa  tsakanin Naira 910 zuwa 950 a kasuwar bayan fage.

Sun kuma yi nuni da cewa an tilastawa dillalan da ke son shigo da man Fetur  dakatar da ayyukansu saboda karancin kudaden kasashen waje.

Dillalan sun shaida wa manema labarai cewa, dan kasuwan nan mai suna Emadeb, wanda ya shigo da man kwanan nan, yanzu ya gagara ya dawo da jarin da ya zuba saboda faduwar darajar Naira.

Jami’in hulda da jama’a na kasa na kungiyar dillalan man fetur, Cif Chinedu Ukadike, ya bayyana cewa a halin yanzu ya ‘yan Najeriya su yi tsammanin karin farashin man fetur nan ba da dadewa ba saboda tsadara chanjin Dala.