Masu sana’ar sayar da iskar gas sun bayyana cewa farashin iskar gas din zai tashi a mako mai zuwa.
Shugaban kungiyar masu sayar da iskar gas ta Najeriya, Olatunbosun Oladapo, ya ce masu amfani da iskar gas din su kwana da sanin cewar farashinsa zai tashi daga mako mai zuwa.
Ya kara da cewa daga cikin dalilan da ya sa farashin zai tashi sun hada da yanayi farashinsa a kasuwannin duniya da hauhawar haraji da tsadar kudin jirage dake dakonsa zuwa kasar nan, sai faduwar darajar naira da sauransu.
Olatunbosun ya bayyana karin farashin da ake shirin yi a matsayin abin takaici.