Babban bankin kasar nan ya alakanta cigaba da faduwar darajar Naira da ake samu yanzu haka, da yadda ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje ke saka kudadensu cikin ma’ajiyarsu ba bisa ka’ida ba.
A yanzu haka dai ana canzar da takardar Dala akan naira 925 a kasuwannin bayan fage.
Mukaddashin Gwamnan babban bankin kasa, Folashodun Shonubi ne ya baiyana haka a Cibiyar Nazari kan al’amuran tsaro ta kasa dake Abuja, A yayin da ya gabatar da wata mukala a jiya.
Ya ce mafi akasarin kudaden da ‘Yan Najeriya mazauna kasashen Ketare ke turowa zuwa kasar nan, suna zuwa ne a Takardun Dala, batare da masaniyar Hukuma ba, wand a hakan ke kara baiwa ‘yan kasuwar bayan fage damar cin kasuwarsu yadda suke so.
Ya ce za’a iya dakile matsalar ne kadai idan har za’a rika turo kudaden a tsarin da ya dace.