Lauya kuma ‘Dan rajin kare hakkin bil’adama Femi Falana na wani gangami da zai sanya duk wani ma’aikacin gwamnati da ke da kalubalen lafiya a yi masa magani a asibitoci mallakar gwamnati a Najeriya.
Mista Falana ya bayyana haka ne yayin wani taro a Legas.
Babban Lauyan na Najeriya na bayar da shawarar a kafa dokar hana duk wani ma'aikacin gwamnati fita kasar waje saboda dalilai na lafiya domin neman magani.
Falana ya yaba wa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo bisa yadda aka yi masa tiyata a gwiwa a daya daga cikin asibitocin kasar nan, ya kuma yi kira ga gwamnati da ta kara maida hankali wajen bunkasa fannin lafiya.
Da ya ke magana akan taken taron, Mista Falana ya ce bai kamata a dauki harkar zaben 2023 a matsayin abin wasa ba.
Ya shawarci jama’a da su kalubalanci ‘yan takararsu daban-daban kan batutuwa masu ma’ana, ganin cewa zaben 2023 ya wuce batun addini da kabilanci.