‘Dan majalisar dokokin jihar Anambra mai wakiltar mazabar Nnewi ta Arewa da Nnewi ta kudu a majalisar wakilai Chris Azubogu, ya bayyana dalilan da suka sa majalisar dokokin kasarnan bata ci gaba da shirin tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari ba sanadiyar matsalar tsaro a Najeriya.
Ya bayyana cewa har yanzu shirin yana nan daram, sai dai yace fa’idar rashin tsige shugaban kasar a wannan lokaci ya fi akasin haka.
Idan za a tuna a ranar 28 ga Yuli na shekarar da muke ciki ne tsagin marasa rinjaye na ‘yan majalisar suka baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari wa’adin makwanni shida akan ya magance matsalolin tsaro a kasarnan ko a tsige shi.
Azubogu ya ce tsige shi abu ne mai wuyar gaske idan aka yi la’akari da yadda aka tsara kasarnan, inda ya ce ‘yan majalisar na kokarin ganin cewa dan takara mai gaskiya da rikon amana ya karbi ragamar mulki a shekarar 2023.