On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Fadar Shugaban Najeriya Ta Kawar Da Yiwuwar Dawo Da Tallafin Man Fetur

Fadar shugaban kasa ta ce babu wani shiri da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke yi na sake dawo da tallafin man fetur.

Babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga Tinubu, Tope Ajayi, ya bayyana haka a lokacin da yake mayar da martani ga wani rahoto da ke cewa shugaban kasar na duba yiwuwar dawo da tallafin  mai na wucin gadi sakamakon tashin farashin mai da kuma farashin canji na kasashen waje.

Ajayi ya rubuta a shafinsa na twitter a daren jiya cewa Tinubu ya gamsu bisa ga bayanan da ke gabansa cewa za’a  iya kula da farashi na yanzu ba tare da sauya manufar tsarin da aka daukkoba a halin yanzu.