A wani yunkuri na ganin an farfado da darajar naira, Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, ta kafa wata runduna ta musamman mai dauke da jami’anta dubu 7 da zasu yi aiki a daukacin ofisoshinta na shiyya guda 14 dake kasar nan, domin kakkabe masu tsuga ma Dala farashin da ya wuce ka’ida.
Wannan mataki na zuwa a yayin da darajar nairar ta sake sauka a jiya Laraba, bayan da aka canzar da Takardar dala daya kan naira dubu 1 da 500 a kasuwannin bayan fage, a yayin a farashinta na hukuma ke kan naira dubu 1 da 418.
Kakakin Hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya ce Hukumar ta gaiyaci masu Jami’oi dake zaman kansu da sauran makarantu dake karbar kudin makaranta da Dala a kasar nan.
Hukumar ta ce ta cafke wasu daga cikin masu makarantun dake karbar kudin makaranta da Dala a jihohin Legas da Ribas domin kare tattalin arzikin kasa.