A yanzu haka, Ana sa ido a kan wasu gwamnonin jihohi uku da ke kan karagar mulki kan yunkurin da suka yi na karkatar da biliyoyin Naira ta hanyar biyan albashin ma’aikata.
Shugaban Hukumar Yaki da masu yiwa Tattalin Arzikin Kasa zagon kasa, EFCC, Abdulrasheed Bawa, ne ya baiyana haka, yayin wata hirarsa da jaridar Daily trust a ranar Alhamis.
Ya ce za a ci gaba da kai samame kan masu sana’ar Canji , inda ya bukaci ‘yan Najeriya da su marawa yunkurinsu baya, domin amfanin kowa da kuma cigaban Najeriya.
A ranar litinin ne, Hukumar ta jagoranci kai sumame kan wasu warure da 'yan canji ke musayar kudi a jahohin kano da Abuja.
Yanzu haka dai farashin naira yana kaiwa sama da 800 akan kowacce dala daya, tun bayan da babban bankin kasa ya bada sanarwar cewa zai sauya fasalin takardun naira na 200 da 500 da kuma 1000.