Hukumar da ke yaƙi da masu yiwa Arzikin Kasa zagon Kasa ta EFCC ta kama wasu mutane da ake zargi da sayen ƙuri'u a yayin zaɓen gwamna a jihar Ekiti.
Hukumar EFCC na cikin hukumomin tsaro da suka aike da Jami'ansu domin Sanya idanu kan yadda zaben ke gudana.
Anyi holen wasu daga cikin mutanen da ake zargi a offishin 'yan sanda na Oke Ori Omi bayan an kamasu da ake zargin suna amfani da su Wajen sayen Kuri'a.
Haka Kuma Jami'an na EFCC sun yi dirar mikiya a wata rumfar zaɓe inda suka yi awon gaba da wasu, sannan an kama wasu mutane a wani gida suna amfani da Littafi wajen lissafa bayanan masu zabe a wani yanki na Jihar.
Dama tun da safiyar ranar asabar wasu daga cikin masu jefa ƙuri'a suke ta kokawa kan yadda suka ce ake sayen ƙuri'u a wasu rumfuna zaɓe.
Wani bidiyo da gidan talabijin na Channels ya wallafa a shafinsa na Twitter ya nuna yadda jami'an EFCC suka yi dirar mikiya a wata rumfar zaɓe inda suka yi awon gaba da wasu.