Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta kama wani Sunday Adepoju, mamallakin gidan shakatawa na De Rock Club da ke Ibadan da wasu mutane 21 bisa zargin damfara ta intanet.
Mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren shine ya bayyana hakan a Ibadan ranar Litinin, yace an kama wadanda ake zargin ne a gidan shakatawar da ke kan babban titin Ring Road a Ibadan a wani samame da jami’an leken asiri suka kai.
Haka kuma an kama wasu ma'aurata Aladenusi Ayodeji da Aladenusi Sadiat wadanda akafisani da Bonnie da Clyde.
Sauran a cewar kakakin EFCC sun hada da Ajuwon Ibrahim da Ogunniyi Stephen da Bolaji Quadri da Olajire Olamilekan da Ojo Kolapo da Kajero Sodiq sai Kareem Abiodun da Bolaji Toheeb da Banjo Toyin da Clement Adeseye da dai sauransu.