Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa EFCC, Ta ce zuwa yanzu ta kwato naira bilyan 30 daga hannun dakataccen babban akanta na kasa, Ahmed Idris, da ake tuhuma da wawure naira bilyan 109.
Shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa ne ya baiyana haka a ranar Alhamis lokacin da yake jawabi, a yayin taron manema Labarai na fadar shugaban kasa, da aka shirya a fadar mulkin kasar nan dake Villa Abuja.
Bawa wanda yayi bayani kan aiyukan da hukumar ta gudanar kawo wannan lokaci a karkashin ikonsa, Ya ce har yanzu hukumar bata janye tuhumar naira bilyan 7 da milyan 100 da take yiwa tsohon gwamnan jihar Abia, kuma Bulaliyar majalisar dattawa a halin yanzu, Sanata Orji Kalu ba.
Ya ce babu kotun data sallami Sanatan ko kuma ta wanke shi daga zargin, a saboda haka har yanzu hukumar EFCC na bin kadin al’amarin.