Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Ta cafke manajan wani banki saboda zarginsa da boye sabbin takardun kudi da aka sauyawa fasali.
Kakakin hukumar Wilson Uwujaren, shine ya tabbbatar da haka a ranar Litinin, duk da cewar bai baiyana sunan manajan bankin da ake zargi da aikata lefin ba.
Ya ce an dakume manajan bankin ne saboda yadda yaki amincewa a saka sabbin takardun kudin a cikin injinan cirar kudi na ATM, duk kuwa da cewar bankin nasa ya samu sabbin kudi har naira milyan 29.
Ya kara da cewar, a lokacin da suka gano an boye sabbin takardun kudin, jami’ansu sun tabbatar da an raba su ga mutanen da suka shafe tsawon lokacin akan layi suna dakon samun kudin.
Daga nan sai yayi kira ga jama’ar kasa, dake shan wahala wajen samun kudinsu a bankunan da suke ajiya, kuma suke zargin a kwai wata ‘kullalliya a ‘kasa, da su gaggauta lalubar hukumar ta EFCC domin yin abunda ya kamata.