Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC , ta ce a yanzu haka tana kan binciken gwamnan jihar Zamfara, mai shirin barin gado, Bello Matawalle saboda zarginsa da yin awon gaba da tsabar kudi, naira da gugar naira har milyan dubu 70.
Shugaban hukumar, Abdul Rashid Bawa ne ya baiyana haka, Ta bakin mai magana da yawun hukumar Osita Nwajahat, yayin wani taron manema labarai da aka shirya ranar Alhamis a Abuja.
Kazalika shugaban hukumar ta EFCC, Ya tabbatar da cewar har yanzu suna rike da tsohon ministan lantarki Sale Mamman, wanda jami’an hukumar suka cafke saboda zarginsa da wawure naira milyan dubu 22.
Bugu da kari shugaban hukumar ta EFCC, ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su maida hankali da kalaman da gwamna ya yi a kwanan nan, wanda yake ganin baikensa bisa zargin cewar ba ya bincikar waziran gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, sai dai gwamnoni.