Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta sake kai karar tsohon gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefeile kara a gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja.
A sabuwar tuhumar, Hukumar na zargin Emefiele da amincewa a buga takarduna kudi na milyan 684 da dubu 590 akan kudi naira bilyan 18 da milyan 96.
Hukumar ta EFCC ta zargi tsohon gwamnan da karya doka domin cutar da jama’ar kasa a yayin aiwatar da shirinsa na canjin kudi a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Hukumar ta zargi Emefiele da cire tsabar kudi naira bilyan 124 da milyan 800 daga cikin asusun tattara haraji na kasa.
Babban mai gabatar da kara na hukumar EFCC, Lauya Rotimi Oyedepo SAN, ya ce za’a gurfanar da Emefiele gaban mai shari’a Hamza Mu’azu kan sabbin tuhume-tuhume guda hudu, wanda suka shafi rashin yin biyayya ga doka, da buga kudi ta haramtacciyar hanya da sauran lefuka.