On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Edwin Clark Na Neman A Cire Wasu Jahohi Uku Daga Hukumar NDDC.

Shugaban kungiyar Pan Niger Delta, PANDEF, Cif Edwin Clark, ya yi kira da a cire jihohin Abia, Imo, da Ondo daga hukumar raya yankin Neja Delta, NDDC.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi gyaran fuska ga doka ta 2000 da ta kafa hukumar.

Clark ya ce gyaran dokar zai bada dammar cire Jihohin da ba na Neja Delta mai arzikin man fetur ba, kamar  Abia, Imo da Ondo daga jihohi tara da suke karkashin  NDDC wadanda su ne, Ondo, Edo, Delta, Bayelsa, Ribas, Imo, Abia, Cross River da Akwa Ibom.

Dattijon wanda ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Talata, ya bayyana cewa shigar jihohin uku a cikin hukumar wata matsala ce ta siyasa.