On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

ECOWAS Tayi Watsi Da Wa'adin Mika Mulki Cikin Shekara 3 Daga Sojojin Juyin Mulkin Nijar

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ECOWAS, ta yi watsi da shirin mika mulki na shekaru uku da gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar ta gabatar.

Jagoran juyin mulkin, Janar Abdourahamane Tchiani, ya yi wata ganawa da tawagar ECOWAS, a ranar Asabar, inda ya yi alkawarin mayar da Nijar bisa tafarkin dimokuradiyya nan da shekaru uku.

Da yake mayar da martani, kwamishinan harkokin siyasa da zaman lafiya da tsaro na ECOWAS, Abdel-Fatau Musah, ya ce ECOWAS bata amince da kudirin ba, wanda ke Ingiza daukar matakin soji.

A wani bangaren kuwa, dubban ‘yan Nijar ne suka cika kan tituna a jiya inda suka bayyana goyon bayansu ga gwamnatin mulkin soji sakamakon yunkurin ECOWAS na mamaye kasar.

A hukumance shugabannin sojoji sun haramta zanga-zangar amma a aikace ana barin masu goyon bayan juyin mulkin su ci gaba da gangami.