Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, a ranar Lahadi, ta yanke shawarar fara tattaunawa da mahukuntan gwamnatin mulkin Soja ta jamhuriyar Nijar, kan gajeriyar taswirar mika mulki, domin saukaka kafa tsarin sa ido da tantance sauyin yanayin da ake ciki.
Ta ce manufar ita ce a gaggauta maido da tsarin mulkin kasar wanda aka hambarar da shugabancin kundin tsarin mulkin kasar a karshen watan Yulin 2023.
Shugaban Hukumar ECOWAS, Dr Omar Touray ne ya bayyana haka a lokacin da ya karanta sanarwar bayan taron shugabannin kasashe da gwamnatoci karo na 64 da ya gudana a dakin taro na fadar gwamnati da ke Abuja.
A taron na ranar Lahadi, kungiyar ta amince cewa kwamitin zai kunshi shugabanin kasashen Togo da Saliyo da Jamhuriyar Benin.