Fitaccen dan wasan kwallon kafa na duniya dan asalin kasar Brazil Pele ya rasu yana da shekara 82 a duniya. Shahararren dan wasan kwallon kafar na Brazil Pele, wanda shine dan wasa mafi girma a tarihi kuma wanda ya lashe gasar cin kofin duniya sau uku ya rasu bayan yayi fama da cutar daji.
'Yarsa Kely Nascimento ce ta sanar da mutuwar mahaifin nasu a shafin ta na Instagram a ranar Alhamis.
Kwamitin shirya wasannin Olympic na duniya, ya nada shi a matsayin gwarzon dan wasan karni a shekarar 1999, Pele shi ne dan kwallon kafa daya tilo a tarihi da ya lashe gasar cin kofin duniya guda uku a shekarar 1958 da shekarar 1962 da kuma shekarar 1970.
Dan wasa Pele da ake yiwa inkiya da Sarki, ya zira kwallaye sama da dubu 1 da 200, kafin ya yi ritaya daga buga tamaula a shekarar 1977.
Nan kuma, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi sahun sauran shugabannin duniya da ‘yan wasan kwallon kafa da ke aikewa da sakon ta’aziyya bisa ga rashin fitaccen dan wasan kwallon kafar Brazil, Pele da aka yi, wanda ya mutu a ranar Alhamis yana da shekara 82 a duniya.
Shugaban kasa, Buhari ya bayyana shi a matsayin wanda duniya ba za ta taba mantawa da shi ba saboda gudunmawar da ya bayar a bangaren wasan kwallon kafa.
Marigayin yayi fama da cutar Koda, da Kansar Hanji, kuma anyi masa tiyata ta karshe a cikin watan Satumbar 2021.
Koda a farkon wannan makon da muke ciki, an ga Pele a cikin wani faifan bidiyo, yana yin sakon bankwana ga iyalansa da abokai da kuma sauran masoya, a yayin da jita-jitar tsanantar rashin lafiyarsa ta yi kamari.