Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II ta mutu tana da shekara 96 a yammacin Alhamis kamar yadda fadarta ta Buckingham ta sanar, yayin da tuni shugabannin kasashen duniya suka fara aike wa ta sakwannin ta’aziyar rashinta.
Sarauniya Elizabeth ta II ita ce basarakiyar da ta fi jimawa kan karagar mulki a tarihin Birtaniya, inda ta gaji karaga daga mahaifinta a shekara ta 1952.
Yanzu haka babban danta Yarima Charles mai shekaru 73, shi ne zai gaji gadon mulkin Ingila kamar dai yadda yake a al’adance.
Daga cikin wadanda suka aike da sakon ta’aziyar har da Sakatre Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, wanda ya bayyana Sarauniya Elizabeth a matsayin wadda ake karramawa a duniya.
Guterres ya ce duniya na girmama marigayiyar saboda karamci da girmamawa da kuma mayar da hankalin da take yi wa jama’a.
Fadar shugaban Amurka ta bayyana matukar kaduwarta da rasuwar Sarauniyar wadda ta bayyana a matsayin shugabar da suke da alaka ta kut-da-kut.
Mai magana da yawun fadar Karine Jean-Pierre ta ce Amurka suna tare da iyalan Sarauniyar da kuma mutanen Birtaniya.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya bayyana marigayiyar a matsayin kawar Faransa, wadda ta bada gudumawa wajen hadin kai da kuma ci gaban Birtaniya a shekaru 70 da tayi tana mulki.
Firaministan Italiya, Mario Draghi ya bayyana marigayiyar a matsayin wadda ta zama alamar Birtaniya da kasashe renon Ingila wajen samar da daidaito da kuma basira.
Sauran shugabannin da suka aike da sakon ta’aziya sun hada da Firaministan India, Narendra Modi da takwaransa na Canada Justin Truduea da shugaban Ireland, Michael Higgins da Firaministan Netherlands, Mark Rutte da shugabar kungiyar Turai Ursula von der Leyen da Sakatare Janar na kungiyar NATO Jesn Stoltenberg.
Su kuwa tsoffin shugabannin kasar Amurka Donald Trump da Barack Obama da kuma tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy da suma suka aike da sakon ta'aziya.