Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU, ta ce ‘ya’yanta ba mabarata ba ne.
Kazalika,Kungiyar Tace dakatar da biyansu albashi da gwamnati tayi ba zai tilasta musu janye yajin aikin da suke yi ba.
Shugaban kungiyar ya kuma yabawa ‘ya’yan kungiyar bisa dattakun da suke nunawa kungiyar duk da wahalhalun da aka dora wa iyalansu sakamakon dokar gwamnatin Taraiyya na ba aiki ba biyan Albashi.
Duk da cewa ana cigaba da tattaunawa kan wasu bukatun kungiyar, shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana fatansa na ganin kungiyar ta samu nasara a gwagwarmayar da take yi.