‘Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu yace duk irin zanga-zangar da ‘yan Najeriya za su yi, gwamnatinsa za ta cire tallafin man fetur idan aka zabe shi ya zama shugaban kasa.
Tinubu ya bayyana haka ne a jiya Alhamis yayin wata liyafar cin abincin rana a jihar Legas tare da matasa masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci da wata kungiya ta shirya domin nazari akan irin gudunmawar da ya bayar a harkar kasuwanci.
Tsohon gwamnan na jihar Legas ya yi mamakin yadda Najeriya za ta rika tallafa wa man fetur ga kasashen Kamaru da Nijar da Jamhuriyar Benin, saboda haka dole ne a cire tallafin.
Haka kuma, Tinubu ya bayyana tsare-tsarensa na sake fasalin kasa da magance rashin tsaro da matsalar tattalin arziki da wutar lantarki da kiwon lafiya da ilimi da karfafa mata da matasa.