Gwamnatin jihar Kano tayi mi’ara koma baya, yayinda ta kammala shiri tsaf domin tarbar shugaban kasa Muhamadu Buhari a yau Litinin.
Shugaban zai zo jihar Kano ne domin kaddamar da ayyukan raya kasa guda takwas.
Idan dai za a iya tunawa a baya gwamna, Abdullahi Ganduje ya rubutawa fadar shugaban kasa wasika inda ya bukaci a dage ziyarar da shugaban kasar domin kaucewa samun matsala yayinda ake cikin matsin chanjin tsaffin kudina Naira.
A cewar gwamnatin, ta damu matuka da irin wahalhalun da ke tattare da karancin lokacin da babban bankin kasa CBN ya bayar na daina amfani da tsofaffin kudaden Naira, da kuma dalilan tsaro.
Wata sanarwa da Abba Anwar, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan ya fitar, ta ce Ganduje ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da masana da ‘yan majalisar dokoki da shugabannin siyasa da ‘yan kasuwa a gidan gwamnati da ke Kano, inda ya kara da cewa an dauki matakin ne domin gujewa duk wani yanayi da ba a zata ba.
Yace, yayin da ake jiran wannan muhimmiyar ziyara, an tsinci kai a cikin wannan hali, wanda ke jefa ‘yan kasa cikin wahalhalu.
Sai dai kuma matakin gwamnatin na Kano na sauya a karshen mako bayan tsawaita wa'adin daina amfani da kudin, inda wata sanarwa daga gwamnatin jihar tace yanzu haka a kammala shirin tarbar shugaban kasar.