Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta yi alkawarin yin bincike kan abunda ya haddasa baiwa Hamatta Iska tsakanin jami’anta da kuma jami’an tsaron gidajen gyaran hali a babbar kotun taraiyya dake Ikoyin jihar Legas, a ranar Talatar data gabata.
Idan ba’a manta ba hatsaniya ta barke jim kadan bayan da kotun ta bada belin dakataccen gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele, tare da bada umarnin cigaba da tsare shi a gidan gyaran hali ,zuwa lokacin da zai kammala cika sharuddan bada shi beli, to sai dai jami’an tsaron farin kaya na DSS sun sake damke shi, tare da yin awon gaba dashi zuwa komarsu.
Mai magana da yawun hukumar, Peter Afunanya ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, Ya baiyana abunda ya faru a matsayin abun ban takaici, wanda ya ce hakan ba kwarewa ba ce a yanayin gudanar da aikin nasu.
Y ace tuni hukumar ta fara bincike kan abunda ya faru.