A jiya ne Tsohon Kakakin shugaban kasa Dr Doyin Okupe, ya aiyana kansa a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar LP.
Ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da gidan talabijin na kasa a jiya.
Idan har abunda ya fada ya tabbata, shine wanda zai yiwa Peter Obi takarar mataimakin shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Sai dai kuma da Yuwar Dr Okupe ya rike matsayin a matsayin na wucin gadi, domin kaucewa saba wa'adin da Hukumar Zabe ta kasa mai zaman kanta ta bawa jam’iyyu, na bayar da sunayen yan takarar shugaban kasa da Mataimakansu.
Har yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance da ta fito daga Peter Obi ko kuma jam’iyyar ta LP