Tsohon tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana kudirinsa na neman zama shugaban kasa a fadar mulki ta White House a shekarar 2024.
Tuni dai tsohon shugaban kasar, ya baiyana burinsa na sake mulkar kasar Amurika a shekarar 2024, inda ya kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa a hukumance, sannan kuma ya mika takarda ga hukumar zabe kasar dake ayyana kansa a matsayin dan takarar shugaban kasa tare da kafa sabon kwamitin yakin neman zabe.
Wannan dai ya biyo bayan zaben tsakiyar wa’adi da aka gudanar a farkon wannan wata da ke nuna cewa ‘yan takarar da ya zaba, sun sha kaye wanda hakan ya yi lahani ga karfin da jam’iyyarsa ke dashi.
A yau ne, ake sa ran, Tsohon shugaban kasar Amurika Donald Trump zai yi jawabi a wani wurin shakatawarsa dake jihar Floridan Amurika.