Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kai tsohon lauyansa kotu kan zarginsa da cin amanarsa dangane da wata kwangila ta dala miliyan 500 da suka kulla a tsakaninsu.
Ya ce lauyan mai suna Michael Cohen ya saba ka’idojin aikinsa na lauya wanda ya kamata yayi amfani da kwarewarsa wajen bashi kariya.
Shari'ar dai ta zo ne a daidai lokacin da abokan Trump ke cigaba da farwa Lauya Cohen, wanda shi ne babban mai gabatar da shaida a binciken da ake yiwa tsohon shugaban kasar a wata kotu dake New York .
Idan ba’a manta ba a makon da ya gabata wani mai gabatar da kara a Manhattan ya tuhumi Mista Trump da aikata lefin zamba cikin aminci ta hanyar da bayar da wasu makudan kudi ga wata jarumar fina-finan batsa.