A cikin wasikar, Shugaban Kasa Buhari, Ya ce gyara
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattijai ta amince da karin kudin biyan tallafin Mai na shekarar 2022 da naira tiriliyan 3 da bilyan Dari 5 da 57, inda za'a samu Karin naira biliyan Dari 4 da 42 da Dubu 72 Wanda zai kama zuwa naira tiriliyan 4.
Kazalika Majalisar dattawan ta kuma karbi takardar da shugaban kasar ya aike mata da ita, inda yake neman majalisar ta amince da Karin ciyo wani bashi domin cike gibin kasafin kudin na shekarar 2022.
Bukatar Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 5 ga watan Afrilun da muke ciki, wadda shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya karanta ranar Talata Yayin zaman majalisar.
A cikin wasikar, Shugaban Kasa Buhari, Ya ce gyara ga tsarin kasafin kudi na shekarar 2022 ya zama wajibi bisa la’akari da sabbin ci gaba da aka samu ta bangaren tattalin arziki na duniya da na Kuma na cikin gida.