Ministan Lafiya na kasa Ali Pate, Ya ce akwai bukatar inganta harkokin kiwon lafiya a kasar nan, tare da kawo karshen fita waje neman magani da ‘yan Najeriya ke
Farfesa Pate ya baiyana haka ne a lokacin da yake ganawa da babbar sakatariya a ma’aikatar lafiya ta kasa, Kachollom Daju, jim kadan bayan shan rantsuwar kama aiki da ya yi a jiya.
Ya koka kan yadda yake ganin tarin ‘yan Najeriya na fita kasashen waje neman magani, Musamman a duk lokacin da ya yi balaguro daga Addis Ababa na kasar Habasha zuwa New Delhi na kasar Indiya.
Sabon ministan Lafiyar ya ce dole ne a inganta tsarin kiwon lafiya na kasa, kuma akwai bukatar bada gudunmuwar duk wani mai ruwa da tsaki ta wannan fanni, domin cimma nasarar da aka sanya gaba.