Hukumar ‘Da’ar Ma’aikata ta kasa, Ta baiyana cewar ya zama wajibi, Zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu Da mataimakinsa Kashim Shettima tare da gwamnoni 28 da aka zaba, su baiyana kadarorin da suka mallaka kafin ranar 29 ga watan Mayu da muke ciki.
Kazalika Sanatoci da sauran zababbun ‘yan majalisar wakilai ta kasa ana saran zasu baiyana dukiyar da suka mallaka kafin ranar 5 ga watan yunin bana, Lokacin da zasu sha rantsuwar kamar aiki.
Mai magana da yawun hukumar, Uwar gida Veronica kato ce ta tabbatar da haka a Abuja , Tana mai cewar baiyana kadarorin ya zama wajibi ga mutanen.
Ta kara da cewar da dama daga cikin wadanda aka zaba sun fara karbar Fom na baiyana kadarorin da suka mallaka a rassan ofishin hukumar dake jihohin kasar nan, kuma ana saran zasu mayar dashi kafin lokacin rantsar dasu.