Farfesan Kimiyyar Siyasa daga jihar Kano Farfesa Kamilu Sani Fage ya ce sabon salon juyin mulki a Afirka zai iya kawo karshen mulkin dimokuradiyya a Nahiyar.
Hakan na zuwa ne biyo bayan juyin mulkin da aka yi a yammacin Afirka da kuma tsakiyar Afirka.
Na baya-bayan nan da sojojin Gabon suka yi, ya sa an yi juyin mulki sau 9 a cikin shekaru uku da suka gabata
Da yake zantawa da wakilinmu Victor Christopher, Farfesa Fage ya bayyana rashin jin dadin yadda dimokiradiyya a Afirka ke samun koma baya.
Sai dai Farfesa Fage ya jaddada cewa, domin hana cigaba da juyin mulki, dole ne shugabannin siyasa su karfafa hukumomin dimokuradiyya, da inganta shugabanci nagari, da habaka tattalin arziki