On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Dole Ne Sai ECOWAS Ta Nemi Sahalewar Majalissar Dinkin Duniya Kafin Afkawa Sojojin Nijar Da Yaki - Falana

Lauyan kare hakkin dan adam Femi Falana ya yi gargadin cewa dole ne kungiyar ECOWAS ta nemi amincewar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin daukar duk wani mataki a Jamhuriyar Nijar.

Gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da wa'adin mako guda da kungiyar ECOWAS bisa jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu, ta bayar a ranar Lahadin da ta gabata na neman a saki zababben shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum tare da mayar das hi kan mulki ya kare a jiya.

Sai dai Falana a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya yi nuni da cewa, ana bukatar ECOWAS ta nemi izinin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin kaddamar da farmaki kan wata kasa mai cin gashin kanta bisa ga sashi na 53 (1) na kundin tsarin majalissar dinkin duniya.