Shugaban hukumar kula da Magunguna ta kasa PCN, Phamasist Ibrahim Baba Shehu Ahmed yace dole ne duk wasu magunguna su tsallake matakin dakin gwaje-gwaje kafin isa wajen masu amfani da su a jihar Kano idan sabuwar kasuwar magunguna ta Kanawa ta fara aiki nan bada jimawa ba.
Babashehu wanda ya bayyana hakan yayin ziyarar karshe ta duba kasuwar, Ya koka akan yawaitar magunguna marasa inganci a budaddun kasuwanni, sai dai yace da zarar kasuwar ta fara aiki al’umma za su samu ingancin magungunan da suke amfani da su tare da kawar da bara gurbi tare da magance shaye-shayen miyagun kwayoyi.
Yace watanni 6 bayan kama aiki amatsayin shugaban hukumar an rufe sama da shagunan magani dubu 3 a sassan Najeriya ta hanyar simame da suke kaiwa na tabbatar da dokokin masana’antar magunguna.
Ya kara da cewa wasu kananan gyare-gyare ne kawai suka rage domin cimma dokoki da ake bukata amma ayyukan kasuwar magungunan sun kammala da ake fatan budewa bada jimawa ba.