Shugaba Bola Tinubu ya ce Najeriya ba za ta dore cikin yanayin tattalin arziki mai rauni ba, wanda ya sa kasarnan ke yin amfani da kashi 90 na kudaden shigarta wajen biyan basussukan waje a cikin kalubalen cigaba.
Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a Abuja yayin da yake bude taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin ta kasa a babban filin wasa na Cif MKO Abiola.
Shugaban ya bayyana cewa dole ne a yanke hukunci mai tsauri domin dora kasarnan a kan hanyar ci gaba, duk da radadin farko da gyare-gyare masu ma'ana ke kawowa.
Tinubu ya bayyana cewa wadatar da ‘yan Najeriya ke bukata zata faru ne kawai da zarar an kawar da talauci daga cikin al’umma tare da hadin gwiwar shugabannin kamfanoni masu zaman kansu na Najeriya.
Ya sake sabunta kudirinsa na tunkarar matsalar albashin jami’an shari’a da masu aiki a bangaren shari’a, inda ya ce dole ne a fara gyaran shari’a na gaskiya da albashi mai kyau da duniya ke tafiya akai da alawus-alawus.