Kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin babbar kotun tarayya akan sashen dokar zabe ta kasa na shekarar 2022
Kotun daukaka kara dake zaman ta a babban birnin tarayya Abuja, a ranar Laraba ta yi watsi da hukuncin da babbar kotun tarayya mai zaman ta a birnin Umuahia dake jihar Abia tayi na rushe sashe na 84(12) na dokar zabe ta kasa ta shekarar 2022.
Yayin zaman ta na yau, kwamitin alkalan mai mambobi uku, karkashin Jagorancin mai sharia Hamma Akawu Barka, ya yanke hukuncin cewa babbar kotun ba tada hurumin sauraron karar tun da fari.
Kotun ta kuma yi bayanin cewa wanda ya shigar da karar, Maduka Edede ya gaza wajen fayyace yadda sashen dokar ya shafe shi, da kuma dalilin da ya sa ya garzaya kotu domin shigar da kara akan batun.
Yayin bayanin ta jim kadan bayan yanke hukuncin, kotun ta kara da cewa mai karar bai bada wani kwakwaran dalili ba kan karar da ya shigar gaban kotun.
Sai dai duk da haka, kotun daukaka karar ta kasa, ta bayyana shakkun ta kan nagartar shashen dokar, wanda tace ya sabawa sashe na 42 (1)(a) na kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999.
Kotun ta soki sashen da yunkurin haramtawa wani bangare na al’umar kasar nan samun damar shiga harkokin zabe da siyasa.