Ministar al’adu ta kasa, Hannatu Musa Musawa, ta magantu akan cece-kucen da ake yin a kasancewarta mai aikin yiwa kasa hidima.
Kakakin hukumar NYSC, Eddy Megwa, yace Hannatu Musawa ta sabawa dokar NYSC kasancewar tana rike da mukamin minista kuma tana hidimtawa kasa, wanda wajibi mutum ya kammala aikin hidimar na shekara 1 kadin karbar duk wani mukami na gwamnati.
Sai dai Ministar ta ce babu wani bangare na kundin tsarin mulki da kuma dokar NYSC da ya ce shugaban kasa ko wata hukuma ba za su iya nada mai yiwa kasa hidima mukaman siyasa ba.
Musawa ta kara da cewa babu wani bangare na dokokin da muke da su da kuma dokar NYSC da suka ce dole ne dan yiwa kasa hidima sai ya kammala kafin a nada shi matsayin siyasa, saboda haka acewarta ba ta karya wata doka ba.