
Shugaban masu rinjaye a zauren majalisar wakilai Alhasan Ado doguwa ya janye daga takarar kujerar kakakin majalisar wakilai ta kasa.
Doguwa ya sanar da janyewar ne a daren jiya, a yayin wani taro da aka shirya tsakanin zababbun ‘yan majalisar wakilai, a otal din Transcorp Hilton dake Abuja.
Ya kara da cewar ya janye daga takarar ne tun daga ranar da jam’iyyar APC ta aiyana Tajudden Abbas da Benjamin Kalu, a matsayin wadanda zasu gaji buzun kakakin majalisar wakilai da kuma mataimaki.
Alhasan Ado Doguwa ya baiyana cewar, Tajudden Abbas ya cancanta kuma yana da gogewa ta sanin yadda zai jagoranci majalisar.
Kazalika y ace ya dauki matakin ne domin nuna goyon bayansa ga zabin da jam’iyyar ta yi, kasancewar shima ya amfana da tsarin nan na shiyya-shiyya wajen raba mukamai.