To sai dai da Alama matakin da uwar jam’iyyar APC ta dauka bai yiwa wasu daga cikin masu neman shugabancin majalisar dokokin ta kasa dadi ba, Inda suka nuna rashin amincewarsu da yin amfani da tsarin ‘yan takara na masalaha
A wani taron manema labarai da suka kirawo a daren jiya, Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Idris Wase, Da shugaban masu rinjaye a zauren majalisar, Alhasan Ado Doguwa,Sunyi fatali da tsarin ‘yan takarar na masalaha, wanda uwar jam’iyyar APC ta kasa ta sanar a ranar Litinin.
Da suke jawabi a wajen taron manema Labaran, Ahmed Wase da Alhasan Ado Doguwa sunce ba zasu kyale a yiwa sabon zauren majalisar dokokin ta kasa zagon kasa ba.
Bugu da kari sun lashi takobin cigaba da takararsu ta neman kujerar kakakin zauren majalisar wakilai ta kasa.