Dillalan mai sun sake hasashen cewar za’a iya samun karin karin farashin man fetur, biyo bayan faduwar darajar Naira kan dalar Amurka.
An dai canzar da Dalar amurika tsakanin naira 900 zuwa 920 a ranakun Laraba zuwa Alhamis.
Dillalan man fetur sun fadawa manema labarai cewar, idan har Farashin Dala ya kai naira 920, To babu shakka farashin Litar man fetir ba zata tsaya akan naira 620 ba.
Shima da yake magana kan batun, Sakataren kungiyar Dillan Man fetir ta kasa masu zaman kansu IPMAN, reshen Abuja da Suleja, Mohammed Shuaibu, ya bayyana cewa kasuwar man fetur tana ta’allaka ne da yadda farashin kudin Dala ya kasance a halin yanzu.