‘Daya daga cikin motocin safar dake dauke da ‘Yan Najeriyar da suka makale a kasar Sudan wadda take kan hanyar zuwa Birnin Port Sudan dake bakin gabar tekun kasar, domin tsallakar dasu zuwa kasar Saudiyya a jiya ta kama da wuta.
Sama da ‘yan Najeriya dubu ne aka kwashe ta hanyar amfani da birnin na Port Sudan, biyo bayan tsauraran sharudda da rukunin farkon na ‘yan Najeriya da aka kwashe ke fuskanta akan iyakokin kasar Masar.
Rahotanni sun baiyana cewar Motocin safa 26 ne suka sauki ‘Yan Najeriyar da suka makale a kasar daga Al-Razi da karfe 12 na daren jiya zuwa gabar tekun kasar, Sai dai daya daga cikin motocin dake dauke da mutane 50 ta lalace sakamakon tsananin zafi da ya yiwa daya daga cikin tayoyin motar yawa.
Daga cikin mutanen dake cikin motar mai suna Sani Aliyu ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an rarraba mutane 40 daga cikin 50 dake cikin motar zuwa cikin sauran motocin Safar, A yayin da ragowar Goman kuma suka shafe daren jiya a wajen da abun ya faru.
Rahotanni sun baiyana cewar daga bisani ‘yan Najeriya sun cigaba da balaguron zuwa gabar birnin.
A yanzu haka dai akwai ‘yan Najeriya masu yawan gaske da suka shafe kimanin kwanaki biyar akan iyakokin kasar Masar, a yayin da jami’an kasar suka hana su shiga cikin Masar wanda ta nan ne jirage zasu dauko su zuwa Najeriya.