On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Darajar Naira Ta Sa Ke Karyewa

NAIRA DA DALA

Darajar naira ta sake sauka a kasuwar bayan fage, bayan da farashin Dala ya yi tashin gwauron zabo zuwa naira 900 akan kowace Dala daya a jiya.

Hakan na zuwa ne kimanin makwanni biyu bayan da aka rika  canzar da takardar dalar akan naira 960 a kasuwar  ‘yan canji ta  bayan fage.

A yan kwanakin baya  darajar naira tad an  farfado kafin daga  bisani  ta koma gidan jiya.

A farkon makon nan an rika  siyar da takardar dala akan naira 850 zuwa 880,  kafin a  jiya  ta tashi zuwa naira  900.