Darajar naira ta sake sauka bayan an canzar da ita kan naira dubu 1 da 234 akan kowacce dala daya a jiya, kamar yadda bayanan canjin kudi suka nuna.
Hakan na nufin darajar nairar ta sauka da naira 65 ko kuma kaso 5 da digo 26 cikin 100, kan yadda aka canzar da ita a ranar juma’a, bisa naira dubu 1 da 169 da kobo 99 akan kowacce dala daya.
Darajar naira ta samu tagoma shi a ranar Larabar makon jiya bayan da aka musayar da ita kan naira dubu 1 da naira 72 da kobo 74, wanda a lokacin yan kasuwar canji sunyi hasashen cewar za’a iya canjar dad ala kasa da naira dubu 1 a karon farko.
To sai dai kuma saukar darajar nairar ta zo daidai da kalaman da gwamnan babban bankin kasa yemi Cardoso ya yi, wanda y ace manufar bankin bas hi kare darajar naira ba,a lokacin da aka yi amsa tambaya ka saukar ma’ajiyar kasar nan ta kasashen waje.