On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Darajar Kudin Kenya Na Faduwa Saboda Rikicin Gabas Ta Tsakiya - Masana

Darajar Kudin kasar Kenya ta karye zuwa wani matsayi da ba a taba ganin  irinsa ba na shilling 150 kan kowacce dala a ranar Litinin.

Wannan lamarin dai ya kara sanya tabarbarewar yanayin tattalin arziki a kasar da ke gabashin Afirka da ke fama da lamuni mai tarin yawa sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.

A cewar babban bankin kasar Kenya, ana siyar da dala kan shilling 150 a ranar litinin, yayin da wasu bankunan kasuwanci da wuraren ‘yan chanji  tuni suka fara aiki da wannan farashin, ko ma sama da haka, a ‘yan makonnin nan.

A cewar wani masani kan tattalin arziki Ken Gichinga, wannan sabon koma bayan da aka samu ya samo asali ne sakamakon karfafa kudin Amurka, saboda rikicin baya-bayan nan a Gabas ta Tsakiya.