
Gwamnatin Tarayya na iya yin Tsumin kusan Naira Trilliyan 7 a duk shekara da kuma Naira trilliyan 35 na jimillhar kashe kudade a kasafin kudi nan da shekaru biyar masu zuwa sakamakon fara aiki da matatar Dangote.
Gwamnan babban bankin kasa CBN, Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin bikin kaddamar da matatar man a Ibeju-Lekki dake Legas.
Ya ce aikin zai samar da wutar lantarki har megawatt dubu 12 kuma zai samar da ayyukan yi kai tsaye dubu 135 da kuma miliyoyin ayyukan yi da ba kai tsaye ba.
Ya kara da cewa, rukunin Dangote ya biya kashi 70 cikin 100 na bashin da ya karba domin gina matatar man.