Magoya bayan jam’iyyar NNPP a nan kano na cigaba da yin zanga-zanga domin kalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, na sauke gwamna Abba Kabir Yusuf na nan jihar Kano daga kan kujerarsa.
A wannan karon, Mata magoya bayan jam’iyyar sun gudanar da tasu zanga-zangar a shalkwatar rundunar yasnandan jihar na kano, domin baiyana hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke a matsayin rashin adalci.
Duk da cewar hukumomin yansanda sun hada gudanar da zanga-zangar, to sai dai a jiya daruruwan mata sanye jajayen kaya dauke da kwalaye da aka yiwa rubutu daban daban, sun gudanar da tattakinsu tun daga gidan sanata Rabiu musa kwankwaso zuwa shalkwatar rundunar yasnandan jihar kano.
Sun bukaci a yi adalci tare da sake jaddada cewar gwamna Abba ne ya lashe zbaen gwamnan jihar kano d aka yi cikin watan maris din bana.
Nan ma a jiya ne, Wasu magoya bayan gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, suka yi dandazo a harabar wasanni ta Lekan Salami dake birnin Badun a jihar Oyo, domin gudanar da addu’o’i tare da gudanar da zanga-zangar lumana domin mika musu bukatunsu na ganin gwamna Abba ya ci gaba da mulkin kano.
Magoya bayan sun fito kan tituna dauke da alluna, da aka yiwa rubuce-rubuce irin su, A yi Adalci a Kano, Kano Abba aka Zaba, Abba ne zabin mu, da sauransu.
Sun gargadi bangaren shari’a kan duk wani abu da zai iya haddasa rikici a Kano da sauran sassan kasar nan.
Da yake zantawa da manema labarai a Badun, mai baiwa gwamnan jihar Kano shawara na musamman kan harkokin kare namun daji, Ahmad Sawaba, ya yi kira ga kotun koli da ta duba hukuncin da kotunan baya suka yanke a tsanake sannan kuma ta yi adalci.