
Ana danganta dan wasan Brazil Neymar da komawa kungiyar kwallon kafa ta Manchester city mai buga gasar zakarun Premier
A cewar wasu rahotanni, yanzu haka mai horasawa Pep Guardiola ya tuntubi dan wasan mai shekaru 31 domin sanin inda ya dosa a kasuwar musayar 'yan wasa mai zuwa.
Kwantiragin Neymar da kungiyar Paris Saint-Germain zai kare ne a shekarar 2027 amma ana rade-radin cewa zai iya canza sheka zuwa gasar Premier.
Kazalika wasu rahotannin kuma na alakanta shi da Manchester United da Chelsea. Yayin da Ita ma Beyern Munich take hakon daukar dan wasan na Brazil.