‘Dan takarar sanata na Jam’iyyar APC a Jigawa, Tijjani Ibrahim ya rasu.
Ibrahim ya rasu ne bayan watanni uku da lashe tikitin takarar Sanata na jam’iyyar APC na Jigawa ta Kudu maso Yamma.
Rahotanni sun bayyana cewa yana kwance a wani asibiti a Abuja inda aka dauke shi zuwa kasar China domin ci gaba da kula da lafiyarsa a lokacin da ciwon ya kara tsanani.
Yana jinyar cutar kafin ya rasu a ranar Asabar a wani asibitin kasar Sin.
Ibrahim ya rasu ne bayan ya lashe tikitin takarar Sanata na jam’iyyar APC inda ya samu kuri’u 361 wanda shi kadai ne dan takara a zaben babu hamayya.
Marigayi Tijjani Ibrahim ya wakilci mazabar Dutse da Kiyawa a majalisar wakilai ta kasa tsakanin 2011 zuwa 2015.
A sakonsa na ta’aziyya, gwamna Muhammad Badaru Abbubakar na jihar Jigawa ya ce ya yi babban rashi tare da Addu’ar Allah ya gafarta ma sa.