Tsohon gwamnan jihar Ekiti Segun Oni kuma dan takarara jam’iyyar SDP ya yi watsi da skamakaon zaben gwamnan jihar da aka kammala a karshen mako.
A ranar Lahadi ne hukumar zabe ta Kasa INEC ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC Bidodun Oyebanji amatsayin wanda ya yi nasara a zaben da Kuri’a dubu 187 da 57 wanda ya doke Oni da ya samu Kuri’a dubu 82 da 211.
Sa’o’i kadan bayan bayyana hakan, Oni ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Mista Moses Jolayemi, ya yi watsi da sakamakon zaben, inda ya ce an yi magudin zabe da kuma sace akwatin zabe wanda ake zargin jam’iyya mai mulki da aikata hakan.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa suna tattara rahotannin kafin yanke hukunci na karshe.