On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

'Dan China Zai Fuskanci Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya A Kano

Marigayiya Ummita da Dan-china

Wata babbar kotun jihar Kano, ta yanke wa wani dan kasar China, Frank Geng-Quangrong, mai shekara 47, hukuncin kisa ta hanyar rataya, bisa samunsa da laifin daba wa budurwarsa ‘yar Najeriya, Ummukulsum Sani, ‘yar shekara 22, wuka ta mutu har lahira a Kano.

Frank, wanda ke zaune a unguwar Railway Quarters Kano, an yanke masa hukunci akan tuhuma guda daya ta kisan kai. 

Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Sanusi Ado-Ma’aji, ya ce masu shigar da kara sun tabbatar da kotu zargin da suke yi ba tare da wata tantama ba. 

Tun da farko, Lauyan masu shigar da kara, kuma kwamishinan shari'a Barista Haruna Isa Dederi, ya shaida wa kotu cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Satumba, na shekarar 2022, a Janbulo Quarters dake Kano. 

Ya ce a ranar da karfe 9 na dare, mai laifin ya daba wa marigayiyar wuka a gidansu da ke Janbulo Quarters Kano bisa wasu dalilai da ba a bayyana ba.

 “An garzaya da wadda aka kashe zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad Kano inda wani likita ya tabbatar da rasuwarta”. 

Wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin. 

Mai gabatar da kara ya gabatar da shaidu shida da za su tabbatar da tuhumar da ake yi wa wanda ake kara da kuma abubuwa 4 da ka iya zama hujja ga Kotu.

A cewar mai gabatar da kara, laifin ya ci karo da tanadin sashe na 221(b) na kundin laifuffuka. 

Lauyan wanda  ake kara, Muhummad Dan’azumi, ya gabatar da wanda ake kara don kare kansa, da kuma masu bayar da shaida guda 5 tare da gabatar da wasu abubuwa biyar da zasu iya zama hujja. 

Da yake kare kan sa,  Frank ya ce, "ban kashe Ummulkhulsum da gangan ba amma na daba mata wuka don kare kaina bayan ta kama min wani bangare na Al'aura.

Ya roki kotun da ta yi adalci da jin kai a hukuncin da zata yanke.

Da take zantawa da manema labarai jim kadan bayan yanke hukuncin, mahaifiyar mamaciyar, Hajiya Fatima Zubairu, ta bayyana gamsuwarta da hukuncin da alkalin ya yanke. 

(NAN)