On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

DAMUNAR BANA: Manoma Na Cigaba Da Kauracewa Gonakinsu Saboda Hare-Haren 'Yan Ta'adda A Jihar Zamfara

Manoma a jihar Zamfara na cikin fargabar yin  noma a bana, saboda  kalubalen tsaro da jihar ke cigaba da fuskanta.

Daya daga cikin manoma a  karamar hukumar Maru, Musa Garba, ya ce a duk shekara yana girbe buhunan shinkafa sama da 100 da buhun gero 50, sai dai ya koka da cewa har yanzu bai yi shuka ba a bana saboda tsoron ‘yan fashin daji da kullum suke mamaye gonaki domin  sacewa  ko kashe manoma.

Shi kuwa wani manomi Sani Musa ya ce ya yanke shawarar yin shuka a bana saboda tunanin cewa gwamnati mai ci za ta dauki mataki cikin gaggawa kan matsalar tsaro. Sai dai ya koka da yadda ‘yan fashin daji  suka lalata amfanin gonakin.

Jaridar Punch ta rawaito cewayanzu hakan anyi watsida  sama da kashi 70 cikin 100 na filayen noma a jihar saboda fargabar ayyukan ‘yan bindiga.