On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Dalilan Da Suka Hana Gwamnatin Jonathan Aiwatar Da Rahoton Taron Kasa Na 2014

Tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan, ya yi karin haske kan dalilin da ya sa gwamnatinsa ta gaza aiwatar da shawarwarin rahoton taron kasa na shekarar 2014.

Ya ce masu zarginsa da kin aiwatar da rahoton na yin hakan ne bisa rashin fahimtar yanayin siyasa a lokacin da kuma tsawon lokacin da ake bukata wajen aiwatar da  rahoton.

Jonathan ya yi bayaninsa ne a wajen gabatar da wani littafi kan taron kasa na 2014 da aka yi a Abuja, ranar Talata.

Tsohon shugaban wanda Tsohon sakataren gwamnatin tarayya Anyim Pius Anyim ya wakilta, ya ce domin aiwatar da rahoton, dole ne sai anyi gyare-gyare da dama a cikin kundin tsarin mulkin kasa wanda alhakin yan majalisa ne.

Idan za’a iya tunawa dai a taron kasa na shekarar 2014 an  ba da shawarwari masu yawa da suka haɗa da raba madafun iko ga jihohi a fannin tsaro da sarrafa albarkatu.